Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Fashewar Tukwanen Gas Ta Raunata Mutane Da Dama Da Lalata Ababen Hawa A Katsina


Katsina
Katsina

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Katsina Abubakar Sadiq shima ya tabbatar da afkuwar lamarin a cikin wata sanarwa.

Mutane da dama sun jikkata sannan ababen hawa 7 da gidaje 2 sun lalace, bayan da wata babbar mota dake dakon tukwanen gas tayi bindiga a karamar hukumar Jibiya ta jihar Katsina.

Duk da cewa ba’a samu asarar rai sakamakon hatsarin ba, wata majiya a yankin, ta shaidawa tashar talabijin ta Channels ta wayar tarho a yau Juma’a cewa ba’a tantance musabbabin fashewar ba.

A cewar majiyar, babbar motar ta taso ne daga jamhuriyar Nijar dake makwabtaka domin kai tukwanen gas din zuwa yankin magamar Jibiya.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Katsina Abubakar Sadiq shima ya tabbatar da afkuwar lamarin a cikin wata sanarwa.

Sadiq ya bayyana cewa al’amarin ya faru ne da misalin karfe 8.45 na safiya sa’ilin da jami’an ‘yan sandan dake aiki a caji ofis din Jibiya suka jiyo karar wata fashewa mai karfi.

Ya kara da cewa, nan take baturen ‘yan sanda mai kula da shiyar Jibiya ya jagoranci jami’ansa da hadin gwiwar sojoji, zuwa wurin da al’amarin ya faru.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG