Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wata Kotu A Pakistan Ta Yi Wa Tsohon Firai Minista Imran Khan Da Matarsa Daurin Shekaru 14 A Gidan Yari


Tsohon Firai Minitan Pakistan Imran Khan (R) da matarsa Bushra Bibi (L) a babban kotu na Lahore
Tsohon Firai Minitan Pakistan Imran Khan (R) da matarsa Bushra Bibi (L) a babban kotu na Lahore

Wata kotun yaki da cin hanci da rashawa a Pakistan ta yanke hukuncin daure Imran Khan da matarsa ​​Bushra Khan na tsawon shekaru 14 kowannensu, bisa zargin sayar da kyaututtukan gwamnati ba bisa ka'ida ba, jam'iyyarsa ta ce a yau, Laraba.

WASHINGTON, D. .C - Wannan shi ne hukunci na uku da aka yanke wa tsohon Firai Ministan kasar cikin 'yan watannin da suka gabata.

Imran Khan
Imran Khan

Hukuncin ya kuma hada da dakatar da shi na tsawon shekaru 10 daga rike mukamin gwamnati, in ji jam'iyyarsa ta Pakistan Tehreek-e-Insaf (PTI).

Jam’iyyar ta PTI ta kara da cewa Bushra Khan, wacce aka fi sani da Bushra Bibi, ta mika kanta domin kamawa jim kadan bayan da aka yanke hukuncin.

Daurin shekaru 14 ya fi tsanani fiye da hukuncin daurin shekaru 10 da aka yanke wa Khan a ranar Talata kan zargin tona asirin kasar, kuma a mako guda kacal kafin a gudanar da zaben kasa. Har yanzu dai ba a bayyana ko hukunce-hukuncen biyu na Khan za su gudana a lokaci guda ba.

"Wannan wata rana ce mai bakin ciki a tarihin tsarin shari'ar mu, wadda ake rushewa," in ji tawagar yada labaran Khan, ta kuma musanta zargin da ake yi na cewa an aikata wasu laifuka.

"Kotun ba ta bada dama lauyoyi su tambayi wadanda ake zargi ba kuma ba a kammala bahasi tsakanin lauyoyin ba aka yanke hukunci ta fito kamar tsarin da aka riga aka ƙaddara a cikin wasa," in ji ta, ta ƙara da cewa "Wannan hukuncin mai ban mamaki ne kuma za a ƙalubalance shi."

Ana tuhumar Khan da matarsa da laifin sayar da kyaututtuka ba bisa ka'ida ba da darajarsu ta kai rupees miliyan 140 ($501,000) mallakar gwamnati kuma sun karba a lokacin da ya zama Firai Minista tsakanin 2018 zuwa 2022.

Imran Khan da matarsa
Imran Khan da matarsa

Jami'an gwamnati sun yi zargin cewa mataimakan Khan ne suka sayar da kyaututtukan a Dubai.

Jerin wadannan kyaututtuka da tsohon Ministan yada labarai ya raba sun hada da turare, kayan ado na lu'u-lu'u, saitin kayan cin abinci da agogo bakwai, shida daga cikinsu kirar Rolex, mafi tsada shi ne "Master Graff Limited edition" wanda darajarsa ta kai rupees miliyan 85 ($304,000).

An kuma yanke wa Khan hukuncin zaman gidan yari na shekaru uku a watan Agusta bisa wannan tuhuma da wata kotu ta yi, amma an dakatar da wannan hukuncin bayan an daukaka kara.

Hukuncin na ranar Laraba ya biyo bayan wani bincike da babbar hukumar da ke yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta gudanar, wato National Accountability Bureau (NAB), wadda ita ma ta tuhumi matar Khan a cikin karar da ta shigar.

-Reuters

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG