Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Imran Khan Ya Tsallake Rijiya Da Baya


Imran Khan - Zanga zangar kin jinin gwamnati.
Imran Khan - Zanga zangar kin jinin gwamnati.

Tsohon Firaimininstan Kasar Pakistan Imran Khan ya samu rauni a wani yunkuri hallakashi a yau Alhamis, yayin da yake jagorantar zanga-zangar kin jinin gwamnati a Islamabad.

Akalla an harbi Shugaban jam’iyyar adawar Pakistan ta PTI mai shekaru 70 da haihuwa da harsashi daya a kafarsa ta hagu, kamar yadda babban mai taimaka masa Rauf Hassan ya tabbatar wa VOA.

Hassan ya kara da cewa, harin da aka kai da bindiga a garin Wazirabad da ke tsakiyar lardin Pujab, ya yi sanadin mutuwar mutum guda tare da raunata wasu da dama.

An kai Khan wani asibiti da ke Lahore, babban birnin Punjab, mai tazarar kilomita 150 daga wurin da aka kai harin, inda likitoci suka ce yana murmurewa, a cewar hadiminsa.

Hotunan bidiyo sun nuna wani dan bindiga yana harbi daga kasa kan Khan, wand ke saman kan wata babba mota da aka hada da nufin jagorantar zanga-zangar.

XS
SM
MD
LG