A wata sanarwa da ta bayar, MDD ta fadi cewa an kaiwa wasu gine-ginen ta guda 4 a Aguelhok hari a lokuta dabam-dabam jiya Litinin, abinda yayi sanadiyyar mutuwar wani sojan wanzar da zaman lafiya daga kasar Chadi tare da raunata wasu su 8.
Sakatare-Janar na MDD Ban Ki-moon yayi kira akan a dauki matakai cikin gagawa akan wadanda ke da alhakin kai wadannan hare-haren, wanda yace sun isa zama laifukan yaki bisa dokar kasa-da-kasa.
Har yanzu dai babu kungiyar da ta dauki alhakin kai harin.
A shekarar 2012 masu ikirarin su yan Jihadi ne suka mamaye bangaren da aka kai harin a arewacin Mali. Matakin soja da dakarun Faransa suka dauka a shekarar 2013 ya fatattaki mayakan sa-kan daga makeken yankin dake a arewacin Mali, amma duk da haka har wayau suna ci gaba da rike wasu sassa ayankin.
Har yanzu kungiyoyin da ke da alaka da al-Qaida na kai hare-hare a yankin, kuma zuwa yanzu a cikin shekarar nan an kashe sojojin wanzar da zaman lafiya na MDD guda 32 a Mali.