Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasu ‘Yan Kunar Bakin Wake Sun Kai Hari Sansanin ‘Yan Gudun Hijira Na Dalori


Ma'aikatan agaji na jiran zuwan gawarwaki wadanda harin Bom din da aka kai a Maiduguri ya hallaka 16, ga Oktoba 2015.
Ma'aikatan agaji na jiran zuwan gawarwaki wadanda harin Bom din da aka kai a Maiduguri ya hallaka 16, ga Oktoba 2015.

Wasu ‘yan kunar bakin wake sun kai hari sansanin ‘yan gudun hijira na Dalori dake garin Maiduguri a jihar Borno, inda suka kashe mutane biyar da runata wasu talatin da tara.

‘Daya daga cikin ‘yan kunar bakin waken ya samu shiga cikin sansanin ‘yan gudun hijira na Dalori, ya kuma tayar da bam din jikinsa wanda ya hallaka mutane biyar da raunata wasu talatin da tara. Ita kuma ‘yar kunar bakin waken ta biyu ta nufi rukunin gidajen Dolari quarters, inda mutanen unguwar suka gano ta har yara suka yi ta jifanta har sai da ta tayar da bam din jikinta ta kashe kanta kadai.

Unguwar Dalori dai tana da tazarar kilomita uku daga jami’ar Maiduguri, jami’ar da a baya ta sha fama da hare-haren kunar bakin wake.

A cewar shugaban hukumar samar da agajin gaggawa na jihar Borno, Injiniya Ahmed Satomi, ya tabbatar da faruwar lamarin inda yace yanzu haka sun ‘dauke duk mutanen da suka sani rauni zuwa asibiti don samun kulawa.

Wannan shine karo na farko da ‘yan kunar bakin waken suka kai hari sansanin Dalori, duk da yake sun zuwa ta bayansa Allah bai basu ikon shiga ba.

Domin karin bayani saurari cikakken rahotan Haruna Dauda.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:32 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG