Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasu ‘Yan Bindiga Sun Fasa Sabon Gidan Yarin Minna


GWMNAN JIHAR NEJA Alhaji Abubakar Sani Bello
GWMNAN JIHAR NEJA Alhaji Abubakar Sani Bello

Wasu ‘yan bindiga da ba’a tantance ba sun kai hari sabon gidan yarin dake Minna inda suka kashe mutane tare da sakin fursinoni da dama

Mutane biyu aka kashe yayinda wasu ‘yan bindiga suka fasa sabon gidan yarin Minna dake jihar Niger.

Cikin daren Lahadi ne ‘yan bindigan suka fadawa gidan yarin bayan an kammala sallar isha’i. Sun hallaka ma’aikacin gidan yarin guda tare da wani farar hula guda.

Wani ganau wanda bai so a ambaci sunansa ba ya yi bayanin cewa, a gidan yarin ake garkame duk wadanda aka yankewa hukumcin kisa saboda haka duk wadanda suka tsere suna jiran kisa ne. An dauresu ne kuma kodayaushe ana iya kashesu.

Mutane biyun da aka kashe, daya ma’aikacin gidan yarin ne dayan kuma dan kabu-kabu ne da ya kawoshi aiki. Yanzu dai an kiyasta cewa wadanda suka gudu cikin wadanda suke daure sun fi wadanda suka saura a gidan kason.

An kawo karin jami’an tsaro a cewar shi ganau din kuma an kama wasu cikin wadanda suka tsere.

Wannan bas hi ne karon farko da aka taba kaiwa gidan yarin hari ba.

Mustapha Nasiru Batsari nada karin bayani a wannan rahoton da ya aiko

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:28 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG