Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

NEJA: Wasu ‘Yan Bindiga Sun Yi Gaba da Babban Jami’in ‘Yan Sandan Garin Sarkin Pawa


Babban sifeton 'yansandan Najeriya, Ibrahim Idris
Babban sifeton 'yansandan Najeriya, Ibrahim Idris

A garin Sarkin Pawa, hedkwatar karamar hukumar Muya a jihar Neja, wasu ‘yan bindiga sun yi awon gaba da babban jami’in ‘yan sandan yankin tare da dogarinsa kuma har yanzu babu labarin inda suke

Wasu ‘yan bindiga sun jefa al’ummar garin Sarkin Pawa, hedkwatar karamar hukumar Muya, cikin zaman zullumi sanadiyar sace babban jami’in ‘yan sandan yankin tare da dogarinsa.

Shugaban karamar hukumar Muya, Yahuza Muhammad Kuti, yace baicin babban jami’in ‘yan sandan da dogarinsa da ‘yan bindigan suka sace akwai kuma wasu mutane hudu da suma an sacesu, kamar yadda ya yi wa wakilin Muryar Amurka Mustapha Nasiru Batsari bayani.

Wasu mazauna garin sun tabbatar da aukuwar lamarin da yammacin jiya.

Gwamnatin jihar ta Neja ta ce ta damu da aukuwar lamarin, a cewar Kanar M.K. Maikundi, wani hadimin gwamnan jihar na mausamman a kan harkokin tsaro.

Sai dai kuma Kwamishanan ‘yan sandan jihar ta Neja ya ki ya yi magana da wakiin Muryar Amurka akan lamarin saboda wai bai san shi ba kuma bashi da lambar wayar wakilin na VOA.

Ga rahoton Mustapha Nasiru Batsari da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:59 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG