Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan hamayya Sunyi Zanga Zanga A Iran


A wan nan hoto masu zanga suke kai doki wani daga cikinsu,yayinda garwar shara take ci da wuta.
A wan nan hoto masu zanga suke kai doki wani daga cikinsu,yayinda garwar shara take ci da wuta.

Litinin ce,dubban magaoya bayan ‘yan hamayya a Iran suka yi zanga zangar nuna goyon baya ga boren da ‘yan Tunisia da Masar suka yi

Litinin ce,dubban magaoya bayan ‘yan hamayya a Iran suka yi zanga zangar nuna goyon baya ga boren da ‘yan Tunisia da Masar suka yi,har kamfanin dillancin labaran kasar ya bada labarin mutum daya ya mutu wasu da dama kuma sun jikkata a babban birnin kasar Tehran.

Shaidu suka ce jami’an tsaro da dama kan Babura sun bazu cikin birnin jiya litinin lokacinda aka gudanar d a zanga zangar duka da dokar hana bore da gwamanti ta aza.Darururwan ‘yansandan kasar sanye da bakaken kayan sarki sun harba borkonon nan mai sa hawaye,da albarusan roba domin tarwatsa gungun masu zanga zanga.

Kamfanin dillancin labaran mai kwariya kwariyar gashin kai,a abinda ta kira “masu cin amanar kasa” sun harbe wani dan kallo har lahira a gangamin da aka yi a Tehran.

Yanar gizon shugaban ‘yan hamayya Mir Hossein Mousavi, ta bada labarin jami’an tsaro sun kama masu zanga zanga da dama. Hukumomin kasar basu tabbatar da labarin garkame mutanen ba.Yanar gizon Mousavi da takwaransa a gwagwarmaya Mehdi Karroubi duk sun bayyana cewa jami’an tsaro sun zagaye gidajensu domin hana su zuwa gangamain masu zanga zanga.Haka kuma hukumomin kasar sun yanke layin woya na gidan Mousavi.

Wasu masu zanga zanga suna cewa “Allah ya gama da dan kama kariya”.Kalamanda masu zanga zanga suka yi amfani da shi kan shugaba Mahmoud Ahamdinejad lokacin zanga zanga d a aka yi a kasar a 2009 kan rikicin zaben kasar.

Sakatariyar harkokin wajen Amurka Hilary Clinton, tace a zahiri kuma kai tsaye Amurka tana goyon bayan hankoron jama’ar da suka basu a titunan Iran a wunin jiya.

XS
SM
MD
LG