Wasu 'yan biyu Brandon da Brandley Deyo, sun yi amfani da na'urar daukar hoto don nuna basirar su a kwallon Kwando a lokacin da suke makarantar sakandare, inda suka saka hotunan bidiyon a yanar gizo da fatan jan hankalin masu daukar 'yan wasan kwaleji. Suka kuma bige da kirkiro wani shafin 'yan wasa matasa da masu goya masu baya da taimakon fitattun 'yan wasan NBA Lebron james, Kevin Duran da sauransu.
Matasan 'yan shekaru 26 da haihuwa yanzu sun kafa shafin yanar gizon mai suna Mars Reel, don nuna hazakar 'yan wasan kwallon kwando na makarantar gaba da sakandire. Ana sa ran wadanda suka fi kwarewa a wani dandalin nuna mutane goma da suka fi a kowane mako, da yake taimakawa 'yan wasan da ba'a sani ba fitowa su zama sanannu a cewar Brandon Deyo.
An fara ne da tunanin nunawa masu daukar 'yan wasan dake shirin shiga kwaleji kwarewar 'yan biyun. Da yake ba zasu iya biyan kudin zuwa samun horo a sansanin 'yan wasan kwallon Kwando masu tsada ba, sai suka sawo na'urar daukar hoto suna daukar wasannin suna aika wa makarantu suga abinda zai faru.
'Yan tagwayen sun shiga Jami'ar Of Maryland, amman suka bari suka shiga kasuwancin su, suka sawa kamfanin nasu suna Mars Reel, wani suna da zai fita daban. A yau suna hulda da 'yan jarida da masu daukar hotunan bidyo labarai 800 a kasashen duniya dabam dabam, suka kuma ce, suna fitar da wasanninsu a tashoshin talabijin masu watsa labaran wasannin.
Facebook Forum