Shugaban tsohuwar PDP Bamanga Tukur da yake mayarda da martani ya ce wanda da suke rike da mukaman siyasa suna iya rasa kujerunsu domin kiran kansu sabuwar PDP. To sai dai kuma gwamnan Sokoto Aliyu Magatakarda Wamako ya ce maganar Bamanga Tukur maganar banza ce domin a majalisar ban da mutane bakwai dake tare da Bamanga Tukur fiye da dari uku suna tare da bangaren Kawu Baraje ne. Ya ce majalisar gaba daya tana tare da su, wato sabuwar PDP.
Idan ba'a manta ba sun cimma yarjejeniyar tsagaita wuta makon da ya gabata har sai sun sake zama 7 ga watan Oktoba to amma furucin Bamanga Tukur da na Aliyu Wamako sun saba ma yarjejeniyar.
Dangane da ko za'a iya shawo kan rikicin jam'iyyar nan da 7 ga watan Oktoba Isa Tafida Yariman Muri dan majalisar zartsawa ta PDP ya ce babu wanda zai samu duk abun da yake so. Ya ce bangaren Baraje ba zasu samu duk abun da suke so ba. Haka ma bangaren shi Bamanga Tukur. Gefen shugaban kasa ba zai samu abun da ya samu da ba. Dole akwai canji. Shi ma gwamna Wamako ya yi tababan yiwuwar samun sulhu. Dalili kwa sun yarda kowa ya kama bakinsa amma sai gashi Bangaren Bamanga Tukur sun shiga yin maganganun banza.
Sale Shehu Ashaka nada rahoto.