Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasu Matasa A Jahar Bauchi Sun Goyi Bayan Karin Kudin Man Fetur


Wasu matasa a jahar Bauchi sun yi zanga zangar lumana domin nuna ra’ayin sun a amincewa da Karin kudin man Fetur da gwamnatin Najeriya ta yi daga Naira tamanin zuwa Naira dari da arba’in da biyar a kowace lita.

Matasan da yawansu ya kusa dari bakwai sun yi tattaki zuwa fadar mai martaba sarkin Bauchi, da gidan gwamnatin jahar, da kuma ofishin kungiyar manema labaran jahar.

Yayin da yake ma manema labarai bayani, mai Magana da yawun kungiyar matasan Dr Danjuma Dabo y ace suna goyon bayan matakan da shugaba Muhammadu Buhari ya dauka domin dan kasa ne na gari, kuma mai kishin kasa.

Ya kara da cewa dama talakawa basu taba cin moriyar tallafin man da ake ta Magana a Najeriya ba, Dabo ya ce akwai lokutan da talakawan Najeriya suka sayi lita guda akan kudi naira dari uku, dan haka a cewar su cire tallafin shine mafi alheri a gare su.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG