Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mata masu Shugabanci Sun Fi Takura Wa Mata Kanana A Wurin Aiki


Shirin mata na wannan makon ya sami zantawa ne da wata matashiya kuma matar aure wadda ta nemi a sakaya sunan ta kuma ta yi mana baya ni akan irin kalubalen da yawancin mata masu aikin gwamnati kan fuskanta musamman wajan mata shugabannin su a wuraren aiki.

Matashiyar ta bayyana cewa bata taba fuskantar irin wannan matsala ba amma ta san mata da dama da suka sami kansu cikin irin wannan yanayi na takura da tsangwama da kaskantarwa daga shugabanni mata kan nunawa mata na kasa dasu.

Ta ce, “Akwai kawa ta wadda ta fara tunanin kamar ta bar aikin da take yi a sakamakon irin takurar da ake yi mata, kuma da farko kafin ta yi aure bata taba fuskantar irin wannan, amma daga lokacin da ta yi aure sai komi ya canza har ma ta fara tunanin barin aikin”.

Matashiyar ta kara da cewa babbar matsalar ma sai mace ta sami juna biyu ko lokacin haihuwar ta ya zo sa’annan suke danne mata hakki kuma lallai wannan bai dace ba domin kuwa a cewar ta, hakan na kashe wa mata da dama gwiwa mai makon karfafa su.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG