Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jerin Wasu Gidaje Masu Tsada A Kasar Amurka Na Shekarar 2016!


2263132 - Praying Time
2263132 - Praying Time

A kowace shekara akan fitar da jerin gidaje da su kafi tsada a kasar Amurka. A shekarar nan wani gida mai girman hekta 3.3 kimanin filin gidaje ashirin kenan. Shine gidan nada dakuna goma sha biyu, a garin Villa Ruchello, a karamar hukumar Santa Monica, ta jihar California. Shine gidan da aka siya kimanin dallar Amurka milliyan $23M dai-dai da naira billiyan hudu da milliyan shida.

Sai gida na biyu da aka siyar da shi akan kudi dallar Amurka, milliyan $22.1M dai-dai da naira billiyan hudu da milliyan hudu. Gidan nada dakuna goma sha shida, gidan na garin Manalapan, a jihar Florida. Gida na uku kuwa shi aka siyar kimanin dallar Amurka, milliyan $21.5M dai-dai da naira billiyan hudu da milliyan biyu.

Shima gadan na garin Montecito, a jihar California. Sai wani gida a gefen teku na Golden Beach, a jiahr Florida, da aka siyar da shi akan kudi dallar Amurka, $21M dai-dai da naira billiyan hudu da milliyan daya. Wadannan suna daga cikin jerin gidajen da su kafi tsada a kasar Amurka a shekarar 2016.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG