Ma'aikatar tsaron Najeriya tare da rundunar sojin kasar suka ca basu ji dadin kalamun da tsohon babban hafsan hafsoshin Najeriya Janar TY Danjuma ya yi ba.
A kalamun nasa Janar TY Danjuma ya zargi sojojin Najeriya da hada baki da 'yan daba da 'yan tawaye da masu aikata manyan laifuka. Kazalika sojojin sun kasa samar da tsaro ga jiharsa ta Taraba.
Ya kira 'yan Taraban da ma sauran 'yan Najeriya da su kare kansu idan kuma suna jiran sojojin ne su kare su saidai su mutu.
Ma'aikatar tsaron Najeriya ta ce kalaman da suka fito daga bakin babban mutum irin Janar TY Danjuma, babban abun bakin ciki ne. Kanar Tukur Gusau mai magana da yawun ma'aikatar ya ce sojojin Najeriya suna aiki tsakanin su da Allah. A cewarsa a arewa maso gabas inda aka kwashe shekaru tara ana fama da 'yan ta'adda an samu ci gaba yanzu. Injishi da wuya a ce sojojin da suke fafatawa da 'yan ta'adda a ce sun dawo suna marawa 'yan ta'adda baya.
Kwararru irin su Abubakar Umar Kari, na ganin rashin dacewar kalamun na Janar Danjuma. Ya ce da kamata ya yi ya bi hanyoyin da suka dace ya gayawa magabata musamman Shugaba Muhammad Buhari, saboda dangantakar dake tsakaninsu.
Amma masanin halayar bil Adama, Farfesa Muhammad Tukur Baba, ya ce jama'a ba lallai ba ne su fahimci kalamun na Janar din ba. Ya da yakamata ya yi shi ne da ya ba da hakurin zama da juna.
Ga haroton Hassan Maina Kaina da karin bayani
Facebook Forum