A karon farko tunda gwamnan jihar Rivers Rotimi Amaechi da shugaba Jonathan suka shiga takunsakar siyasa wadda ta kai ga gwamnan barin jam'iyyar PDP zuwa ta APC bangarorin biyu sun soma yin cacar baki.
Gwamnan ya fito bainar jama'a yana zargin sunasa ne na daya a jerin sunayen mutane dubun da tsohon shugaba Olusegun Obasanjo ya ambata a waskiarsa cewa shugaba Jonathan na shirin hallakawa domin wata mnufar siyasa. Gwaman ya ce idan mutum nada Ubangiji to haka asirin makiyansa zasu dinga tonuwa. Ya ce idan lokaci ya yi zai yi bayani dalla-dalla tre da bada hujjoji.
Sai dai mai ba shugaba Jonathan shawara kan harkokin siyasa ya ce zargin Amaechi bashi da tushe blantana gaskiya. Ya ce wasikar da Olusegun ya rubutawa shugaban kasa bata da tushe kuma ba gaskiya ciki. Ya ce shugaban kasa ya mayarda martani kuma ya ce idan Obasanjo ya san Ubangijinsa sai ya kawo hujjojinsa domin tabbatar da abubuwan da ya rubuta a wasikar. Shugaban kasa ya umurni jami'an tsaro su binciki maganar kuma ya gayawa Human Rights su ma su yi bincike. Ya ce Amaechi mutum ne wanda za'a ce tamkar kusoshin kansa sun kunce, wato ya soma hauka ke nan.
Wani Bello Abubakar da kan yi nazari kan harkokin siyasa ya yi tsokaci. Ya ce zargin da Amaechi ya yi abu ne na siyasa wanda idan aka cigaba a hakan ba zai haifi da mai ido ba. Siyasar ma kanta za'a yita ne kawai amma mutane ba zasu ci gajiyarta ba domin shugabannin da yakamata su taimakawa jama'a domin su samu cigaba sun shiga wani halin da ba zai anfani kowa ba. Ya ce ita siyasa ba za'a hana zargi ba amma ba irin wannan ba.
Ga rahoton Lamido Abubakar.