Kungiyar matasan arewa ta Northern Youth Progressive tace masu kiran a raba kasa gida biyu ba su fahimci abun da ake nufi da taron kasa ba
WASHINGTON, DC —
Wata kungiyar matasan arewa da ake kira Northern Youth Progressive da Turanci tace bahaguwar fahimtar da wasu 'yan Najeriya suka yiwa taron kasar da ake shirin yi a Najeriya ita ce dalilin su na cewa a raba Najeriyar gida biyu. Wakilin Sashen Hausa a Kaduna, Isah Lawal Ikara, ya ce shugaban kungiyar matasan ta Northern Youth Progressive, Barrister Abubakar Aminu Kurawa ya yiwa manema labarai bayani a garin na Kaduna inda ya shaida mu su cewa haramun ne a doka ma wani dan kasar yayi kiran cewa a raba Najeriya gida biyu.