A jawabinsa na taya murna da jama'ar kasar Najeriya shugaba Jonathan ya sanarda kafa wani kwamitin shirya taron kasa da ya kunshi mutane goma sha uku. Domin samun karin haske dangane da sahihin aikin da kwamitin zai yi abokin aiki Aliyu Mustapha ya zanta da sakataren Dr. Akilu Indabawa. Ya ce aikin da aka basu shi ne a shirya taron kasa yadda za'a duba makomar kasar. Ya ce ana sane da yadda 'yan Najeriya suka damu da alamura da suke gudana a kasar. Wasu sun nemi a bar kowa ya ci gashin kansa kaman irin su kasashen Togo da Kwango da dai wasu. Wasu kuma sun nemi wani abu daban. Don haka ana son kwamitin ya duba kana ya bada shawara kan matakan da yakamata a dauka.
Dr. Indabawa ya ce basu ne zasu tattauna ba kan hanyar da kasar yakamata ta bi. Nasu aikin shi ne su nemi ra'ayoyi kana su ba gwamnati shawarar yadda za'a shirya taron kasa da zai yi nasara. Ya ce basu da abun da zasu ce kan wadanda zasu halarci taron kasar. Ba su ba ne zasu tattauna su ce ga abun da za'a yi ba. Nasu kawai su bada shawara yadda za'a shirya taron.Amma zasu fitar da yanayi mai kyau yadda taron zai ba 'yan Najeriya dama su tattauna da makomar kasarsu game da alamura dake faruwa.
Bukatun masu so a yi taron sun sha karo da juna. Akwai masu son a yi shi domin kasa ta tarwatse kowa ya yi gaban kansa.Da aka tambayeshi cancantar taron ganin irin wadannan ra'ayoyi sai ya ce shi ba zai yanke hukunci ba domin kila shugaban kasa ya ga yakamata a yi taron bisa ga alamuran dake faruwa.
Ga karin bayani.