Yayin da ake shirin kammala matakin farko na gasar cin kofin kwallon kafa ta duniya ta mata da ake yi a Canada, ‘Yan matan Amurka na bukatar su yi kunnen doki ne kawai a wasansu da za su kara da takwarorinsu na Najeriya a yau, domin shiga zagaye na biyu.
Sai dai ana su bangaren, koda sun sami maki ukun da ake bukata, ba lallai ba ne ‘yan wasan Najeriya su samu damar tsallakawa zuwa zagaye na gaba, yayin
da suke da maki daya kacal a gasar.
Wasan dai na nuna alamun mai yiwuwa ‘yan wasan Amurka su yi galaba akan Najeriya, saboda maki hudu da Amurkan ke da shi a wasannin hudu da suka samu nasara, inda kuma suka zira kwallaye 16 yayin da aka zira kwallaye biyu kacal a ragarsu.
A dai haduwarsu ta karshe a shekarar 2007, Amurka ta doke Najeriya da ci daya mai ban haushi.
Sauran wasannin da za a buga a yau sun hada da wasa a rukunin Da ko kuma group D, inda Sweden za ta kara da Australia.
A rukunin C ko kuma group C, Japan ce za ta kai ruwa rana da Ecuardor yayin da Kamaru za ta fafata da Switzerland.