Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wani Matashi Zai Kwashe Tsawon Lokaci A Gidan Yari


Wata kotun majistare a Ibadan ta yankewa wani matashi mai suna Muyideen Nasiru, zaman sheakra uku da wata uku a gidan yari, biyo bayan samun shi da laifin satar kofofi da wasu kayayyaki da suka kai Naira dubu dari biyar 500,000 na wani Coci.

An dai sameshi da laifin hada baki shiga ba bisa ka’ida ba da kuma sata, ya same watani uku, a laifin farko, nabiyu watani goma sha takwas hakama na uku watani goma sha takwas, amma duk zasu tafi bai daya ne ma’ana zai yi watani goma sha takwas Kenan a gidan yari.

Mai shara’a O.K. Omotosho, da yake yanke hukuncin bayan da Nasiru, ya amsa laifinsa, yace mai laifin zai yin wa’adinsa ne a gidan yarin Agodi dake birnin Ibadan.

Ya kara da cewa matashi barawo ne kuma lallai yana da ubangida da yake sayen kayan daga gareshi.

Yana mai cewa zaman irinsu cikin al’uma bashi da alfanu gara ya kasance a gidan yari ko zai koyo hankali daga can.

Tun farko mai gabatar da karar Mr. Olalekan Adegbite ya ce laifin ya sabawa sashe na 390 sakin layi na 9, da 415 da kuma 516 na kundin laifuffuka na jihar Oyo, wanda kuma ya yi tanaji hukunci a cikinsa.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG