An umarci matasa da su kasance masu sanin abinda zasu iya wanda kuma zai kasance mai alfanu ga jama’a masamman abinda ya shafi aiki, kamar yadda wata matashiya Fiddausi Sani, ta furta a lokacin wata hira da wakiliyar Dandalinvoa Baraka Bashir.
Matashiyar ta kara da cewa, an bata gurbin wasu ayyuka a harkar koyarwa amma bata karba ba kasancewar bata da salo da dabarar yi wa dalibai bayanin darrusan da zata koya musu ba wai don ta raina sana’ar koyarwa ba.
Fiddausi ta kuma ja hankalin matasa da su maida hankali su nemi ilimi sannan su dogara ga sana’ar hannu duba da cewar aiki ya zama dan sarki a yanzu,
Ta ce karanci harshen Turanci a yayin da ta nemi gurbin karatu a wani kwas da bata samu ba aka kuma bata harshen Turanci, kammalawarta ke da wuya aiki ya ci tura
Babban burinta a yanzu bai wuce na bude gidan dinki wanda zata kawata shi daidai da zamani, tunda aikin gwamnati ya gagara samuwa in ji Fiddausi Sani Rashidi.
Facebook Forum