Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasu Samari 6, Sun Gudanar Da Binciken Manazarta Sararrin Samaniya


Tawagar matasa shida manazarta sararrin samaniya, sun bayyana bayan kwashe tsawon watanni takwas 8, a cikin sararrin samaniya. Matasan da suka hada da samari hudu, da ‘yan mata biyu. Babban abu da manazartan suka sa a gaba shine.

Bincike don ganin yadda rayuwar ‘yan sama jannati take a yayin da suke cikin duniyar wata, wanda suke daukar tsawon lokaci, batare da iyalai ko wasu abokan magana ba, kasancewar wata rayuwace ta kadaici.

Tun a watan Janairu na wannan shekarar manazartan suka bace, a iya tsawon lokacin, basu da wani abinci baya ga abinci da suka shafin dangin ganye, abubuwan marmari, babu wani abinci mai nauyi, a tare da su.

Sun maida hankali wajen fahimtar wane irin mutane ya kamata a dinga turawa sararrin samaniya, don gudanar da aikin bincike, da duba ga irin yadda rayuwar take, kana da yadda kwakwalwar dan’adam take wajen juriya ga wata rayuwa da bata saba da ita ba.

Sakamakon binciken su, zai taimaka matuka wajen zaben irin mutane da suka kamata a tura irin wannan aiki, da tunanin samu sakamako da zai amfanar da hukumar binciken sararrin samaniya ta NASA, dama duniya baki daya.

Hukumar ta NASA na shirye-shiryen tura mutane, bangaren da akema lakani da ‘Red Planet’ a shekarar 2030 zuwa tsakiyar duniyar wata. Idan aka yi la’akari da yunkurin matasan, za’a ga cewar wata gudunmawace da matasa a koina ya kamata su bada wajen zurfafa bincike don ciyar da kasa gaba.

Akwai bukar matasa a ko’ina suyi koyi da irin wannan dabi’ar ta kishin kasa, daga zaratan matasa, da suka bada kansu wajen gudanar da binciken.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG