A shirinmu na masu kananan sana’oin a yau DandalinVOA ya samu bakunci Malama Hadiza Nura, mai aiki a gidan mai a matsayin mai bada man fetur ga ababan hawa wato 'Feul attendant waccen ta ce ta kama aikin ne domin tallafawa maigidanta da harkokin yau da kullum
Hadiza ta ce babban kalubalen da take fuskanta a wannan harka dai bai wuce yadda akan sami rashin fahimta daga al’umma ba mussamam idan akayi rashin sa’a akwai cincirodun mutane a mafin yawan lokutan sukan gaya mata magana mara dadi da ya jibanci na rashin da’a.
Ta kara da cewa, aikin Fuel attendant aiki ne mai tsamatsi kasancewarta mace kuma a kullum ana yi wa kwastoma abinda yake so ko dai zai saba mata, mussamam a wannan lokaci da wuyan mai ya fi tsanani.
Ta ce dalilin da ya sa ta tsunduma sakamakon matsin tattalin arziki da kasa ke ciki kuma ta lura da cewar hidimomi sun yi wa maigidanta yawa, sannan tana kashewa kanta wasu kananan bukatu, da kauda yawan a bani- a bani
Ta ja hankalin mata mussamam matasa da su nemi na kansu zaman jira ba nasu ne ba, tare da cewar sana’ar hannu maganin takaicin zaman duniya ne.
Facebook Forum