Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wani Jirgin Ruwa Da 'Yan Tawayen Houthi Na Yemen Suka Kai Wa Hari Ya Nitse A Tekun Bahar Maliya


Houthis na Yemen sun ce sun kai hari kan jiragen ruwa uku a kogin Bahar Maliya
Houthis na Yemen sun ce sun kai hari kan jiragen ruwa uku a kogin Bahar Maliya

Wani babban jirgin ruwan dakon kaya ya nutse 'yan kwanaki bayan wani harin da 'yan tawayen Houthi na Yaman suka kai masa, kuma ana kyautata zaton harin ya kashe wani mutum a cikin jirgin, a cewar hukumomi da safiyar Laraba, wanda shi ne jirgi na biyu da ya nutse sanadiyyar hare haren 'yan tawayen.

Nutsewar jirgin mai suna Tutor a Tekun Bahar Maliya ya yi kama da mafarin kara tsanani a irin matakan da 'yan Houthis masu samun goyon bayan Iran su ke daukawa na auna jiragen ruwa a muhimmiyar mashigar ruwa a yakin Isra'ila da Hamas a zirin Gaza.

Harin dai na zuwa ne duk da kwashe tsawon watanni da Amurka ta yi ta na jagorantar wata hobbasa ta tsaro a yankin da ya sa sojojin ruwan kasar ke fuskantar yakin ruwa mafi muni tun bayan yakin duniya na biyu, inda ake kai hare-hare kusan kullum kan jiragen ruwa na kasuwanci da na yaki.

The Liberian-flagged, Greek-owned-and-operated Tutor sank in the Red Sea, the British military’s United Kingdom Maritime Trade Operations center said in a warning to sailors in the region.

Tutor mai dauke da tutar Laberiya, mallakin kasar Girka kuma mai sarrafa kansa ya nutse a cikin tekun Bahar Maliya, in ji cibiyar kula da harkokin kasuwanci ta ruwa ta sojojin Burtaniya a cikin wani gargadi ga ma'aikatan harkokin tekun yankin.

-AP

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG