Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasu Kasashen Afirka Na Tunanin Fara Ajiya a Takardar Kudin China


Takardar kudin China (Yuan)
Takardar kudin China (Yuan)

Yayin da wasu kwararru ke kaffa-kaffa da takardar kudin China, wasu kasashen Afirka na tunanin fara ajiyarsu ta kasashen waje a takardar kudin Chinar.

Kasashen Afirka fiye da 10 na nazarin fa'ida ko rashin fa'idar amfani da takardar kudin kasar China (wato yuwan) wajen yin ajiyarsu ta kasar waje, kamar yadda jami'an kasashen su ka tattauna a watan jiya a birnin Harare na kasar Zimbabbwe.

Amfani da takardar kudin Chinar zai saukaka ma kasashen na Afirka biyan kasar China basussukan da ta ke binsu.

To amma kuma hakan na nufin dogaro ga wani irin tsarin tattalin arziki da cigaba da ke dada fuskantar kokwanto, saboda irin ka'idojin da ya ke amfani da su musamman wajen yin harka da kasashen Afirkan.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG