Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce gwamnatinsa ta gano masu daukar nauyin fafutukar ballewa daga kasar a yankuna daban-daban, da suka hada har da wani dan majalisar dokoki.
A cikin jawabinsa na bikin ranar samun ‘yancin kai na wannan shekara ta 2021, Buhari ya sha alwashin cewa za’a hukunta duk masu hannu a hura wutar rikicin ballewa da dukan masu neman kawo cikas ga sha’anin tsaron kasar.
Buhari ya bayyana yadda jagororin fafutukar ballewa suka arce suka buya a kasashen waje, yayin da suke tunzura matasa da ke cikin kasar suna ta da zaune tsaye da tashe-tashen hankula, yana mai bayyana sunayen jagoran kungiyar IPOB mai fafutukar kafa kasar Biyafara, Nnamdi Kanu, da kuma jagoran fafutukar kafa kasar Yarbawa, Sunday Igboho.
Ya ce “kama Nnamdi Kanu da Sunday Igboho da aka yi a kwanan nan, da kuma binciken da ake ci gaba da yi, sun bayyana cewa akwai wasu manyan mutane da ke daukar nauyinsu. Muna bin sawun wadannan manyan mutanen, ciki har da wani da aka gano cewa dan majalisar dokokin Najeriya ne mai ci yanzu.”
Duk da yake dai bai bayyana sunan dan majalisar ba, Shugaba Buhari ya ce wannan babbar manuniya ce ta yadda wasu shugabanni a kasar suke watsar da hakkokin shugabanci da suka rataya a kan su, domin biyan wasu bukatu na son ran su.
“A maimakon yin kira da karfafa hadin kai, wadannan shugabannin sun raja’a ne kawai wajen kashe makudan kudade domin dora matasa kan mummunar turba ta aikata miyagun laifuka, da kuma ke haifar da rasa rayuka da dukiyoyi.”
Buhari ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta bi hanyoyin da suka dace wajen tabbatar da inganta sha’anin tsaron kasa, ciki ko har da fadakar da jama’a da hadin gwiwa da wasu kasashen waje.
Haka kuma ya ce gwamnati za ta ci gaba da kokarin kawar da duk wani yanayi da zai ba da damar aikata miyagun laifuka, da daukar nauyin ta’addanci a kasar.
Jawabin Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari A Taron Majalisar Dinkin Duniya