Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Masu Fafutukar Kafa Kasar Yarbawa Sun Bata Rawarsu Da Tsalle – Gwamnatin Najeriya


Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari (Facebook/ Muhammadu Buhari)
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari (Facebook/ Muhammadu Buhari)

Ita dai kungiyar ta IPOB ta sha musanta hannu a kisan jami’an tsaron Najeriya da hare-hare da ake kai wa a kudu maso gabashin kasar.

Gwamnatin Najeriya ta ce ta yi mamaki da ta ga masu fafutukar neman kafa kasar Yarbawa sun hada kansu da kungiyar IPOB wacce ta ayyana a matsayin ta 'yan ta'adda.

Wata sanarwa da fadar shugaban kasar ta fitar ta hannu kakakin Buhari, Malam Garba Shehu a ranar Laraba ta ce, ganin masu neman kafa kasar ta Yarbawa suna mara baya ga kungiyar ta IPOB a gangamin da suka yi a New York abin damuwa ne.

A ranar Talata, masu neman kafa kasar Biafra da kasar Yarbawa mazauna Amurka suka yi wani gangamin a kofar hedkwatar Majalisar Dinkin Duniya yayin da aka fara taron majalisar na shekara-shekara a birnin New York na Amurka.

An ga masu gangami dauke da kwalaye da aka yi rubutu iri-iri wadanda ke neman a sawwake masu zama a Najeriya.

Sai dai ga dukkan alamu, hadakar kungiyoyin biyu a kofar zauren majalisar, bai yi wa gwamnatin Najeriya dadi ba.

“Abin mamaki ne a ga masu fafutukar kungiyar “Yoruba Nation” suna marawa kungiyar IPOB baya. IPOB, kungiya ce da aka ayyana ta a matsayin ta ‘yan ta’adda. Ta bayyana kafa kungiyoyin tsaro dubu 50,0900” Malam Garba Shehu ya ce cikin sanarwar.

Wannan hadaka da kungiyoyin suka yi a cewar gwamnatin Najeriya, abin damuwa ne, duba da yadda kungiyar ta “Yoruba Nation” take yawan ta da husuma a gangaminta na kwanan nan.

A cewar sanarwar, kungiyar ta sha kashe jami’an tsaro da fararen hula da babu ruwansu, musamman a wannan shekara yana mai cewa a halin da ake ciki, tana kokarin hana ‘yan Najeriya yin walwala ta hanyar kafa dokar zama a gida a wasu jihohi.

Ita dai kungiyar ta IPOB ta sha musanta hannu a kisan jami’an tsaron Najeriya da hare-hare da ake kai wa a kudu maso gabashin kasar.

“Babu shakka, ‘yan Najeriya da daukacin duniya, za su rika kallon kungiyar ta Yoruba Nation da irin idon da suke kallon wadanda take mu’amulla da su.

“Babu wanda zai dauki wata kungiya da muhimmanci, muddin tana mu’amulla da IPOB.” In ji fadar shugaban kasa.

XS
SM
MD
LG