A mafi yawan lokutan ina wakokin fadakarwa da suka shafi mu’amala tsakanin iyaye da ‘ya'yan su wato hakkin da ke tsakanin ‘ya'ya da iyaye inji mawaki Ibrahim Sale Abdullahi wanda aka fi sani da Ibrahim Mali Dala
Ya bayyana haka ne a yayin da yake zantawa da wakiliyar DandalinVOA kuma ya bayyana cewa abinda ya sa ya zabi bangaren fadakarwa tsakanin iyaye da ‘ya’yansu shine duba da yadda wasu iyayen ke halin ko in kula da rashin damuwa da dabi’un da ‘ya’yansu ke cike ba.
Mali Dala, ya kara da cewa haka zalika wasu yaran da zarar sun girma basa damuwa da irin halin da iyayensu ke ciki, wanda hakan na cikin dabi’a mara kyau, dan haka baya ga wakokin fadakarwa yana wakokin fim ko na tallace-tallace da suka danganci na biki ko suna ko ta ‘yan siyasa
Daga karshe Ibrahim ya ce babban abinda ke ci wa mawaka mussamam masu tasowa tuwo a kwarya shine yadda da kudinsu wasu lokutan idan suka je studio domin rera wakokinsu sai a dinga yi musu kallon da bai dace ba ko wasu dabi’un da bai kamata wanda hakan na kawowa harkar tsaiko ko yana ci masu tuwo a kwarya.
Facebook Forum