Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya bukaci a sake nazarin ka’idojin safarar albarkatun man fetur a Najeriya.
A sanarwar da ya wallafa a shafinsa na X a jiya Laraba, dan takarar shugaban kasar karkashin inuwar jam’iyyar PDP a zaben da ya gabata, yace wajibi ne kasar nan ta koma amfani da jiragen kasa wajen safarar abubuwa masu saurin kama wuta irinsu fetur da man dizel a fadin Najeriya.
“Lokaci ya yi da zamu koma amfani da hanyoyi na daban, irinsu layin dogo, wajen yin safarar albarkatun man fetur a fadin Najeriya.
“Haka kuma yana da muhimmanci mu baiwa direbobin dake dakon irin wadannan kaya masu saurin kama wuta horo tare da sake nazarin ka’idojin safarar albarkatun man fetur da sauran abubuwa masu saurin kama wuta.”
A jiya Laraba an birne fiye da mutane 140 da hatsarin fashewar tankar fetur ya rutsa dasu.
Kimanin wasu mutane 90 da mummunan hatsarin ya rutsa dasu na samun kulawar likitoci a asibitoci daban-daban dake jihar.
Fashewar ta afku ne da tsakar daren Talatar da ta gabata lokacin da tankar ta kwace daga hannun direbanta, wanda ya taso daga kano zuwa garin Nguru a jihar Yobe, a kusa da jami’ar Khadija, dake garin Majiya.
Dandalin Mu Tattauna