To dama idan ana lura, jihohin arewacin Najeriya na daga cikin wadanda suka ci baya a neman ilimin zamani. Sashen Hausa ya tattauna da mataimakin gwamnan Jihar Mallam Ibrahim Wakkal.
“Wato inda matsalolin suke na farko mun binciko wasu, sai muka ga abinda ke gare mu, muna ta kokari mu biya bashin farko, sannan sai muka dawo muna cika na baya. To muna tattaunawa da hukumar WAEC” a cewar Mallam Wakkal.
“Bana a duk Najeriya an samu matsala ta kudi kowa ya san wannan, saboda haka sai ya kasance sun rike sakamakon jihohi da dama”.
Ko ina ilimin zamani ya nufa a jihar Zamfara?
Mataimakin gwamnan yace “abuda zan iya cewa shine Jihar Zamfara kamar wasu Jihohin arewa akwai cibaya kwarai da gaske a bangaren ilimi na zamani.