Alhaji Muhammad Musa Katsina kwamishanan 'yansandan jihar Oyo yace bayan aika aikar sun shiga aiki ainun wajen gano wadanda suka kashe masu jami'i mai suna Ikeoku Nwogu DPO din wata unguwa.
Yace wadanda suka haddasa hargitsi cikin unguwar da wanda suka yi harbi har suka kashe DPO Ikeoku Nwogu duk sun kamasu. Wadanda ma suka gudu zuwa wasu garuruwa daban an kamosu an tasa keyarsu zuwa Ibadan babban birnin jihar Oyo.
Alhaji Musa ya ja kunne mutane. Yace babu wanda zai ga dan sanda na aikinsa yace zai tada rikici har ma ya hallaka dan sandan. Ba zasu bari mutanen da suka yi hakan ba su tsira.
Kawo yanzu sun kama mutane 49 har da mace daya wadda ita ce ta haddasa rikicin. Ita ta je wurin DPO tace danta ya bace kuma ta gano inda ake yanka mutane. Ita ce umalubaisan abun da ya faru. Ita ce ta bada ishanar da aka yi anfani da ita aka kone DPO din.
Ga rahoton Hassan Umaru Tambuwal.