Hafsan-hafsoshin sojojin kasar Pakistan Genaral Qamar Javed Bajwa, yayi tsokaci akan irin rawar da Makaratun Allo ke takawa a kasar, musamman wajen maganace matsalar ta’addanci.
Wannan wata magana ce da babu wanda ke son tabawa, kasancewar ta maganar da ta shafi addini, Mr. Qamar, yayi maganar ne a loacin wani taron karama juna sani da aka gudanar, tare da hadin gwiwar gwamnatin kasar Amurka da ta Pakistan, da niyyar kawo karshen ta’addanci, inda ya ce, wacce irin rawa makarantun Allo ke takawa wajen yaki da ta’addanci, a wannan karni na 21, shekarun kimiyya da fasaha?.
Ya kuma kara da cewa ganin yadda makarantun basa amfani da kayan zamani wajen ilmantar da daliban su, musamman yadda zasu sami damar kwarewa da wayewar zamani, sanin makamar kwamfuta da dai makantan su.
Ta dalilin haka ne ake a cewar sa ake samun damar sauyama matasa tunani, da zasu shiga aikin ta’addanci saboda rashin ilimin zamani da duniya take ciki. Ya kara da cewar, wadannan makarantun basu koyar da wani ilimi baya ga ilimin addini.
Jami’in ya bayyana cewa akwai bukatar surka ilimin addinin da na zamani, don samun rayuwa mai inganci ga matasan gobe, ya kara da cewar, ya samu labarin akwai Almajirai a kasar da su kafi karfin milliyan 2.5, akwai kuma adaddin makarantun Allo sama da 35,337 duk a cikin kasar ta Pakistan.
A bangare daya kuma malaman addinai a kasar na ganin cewar, ba kawai rashin mayar da hanyar koyarwar irin ta zamani ke samar da ‘yan ta’adda ba, suna ganin cewar ko wadanda suka sami ilimin zamani suna shiga wannan munmunar akida, domin kuwa akwai matasa masu irin wannan akida da sun kammala makarantun jami’o’i kamar su Jamai'ar Karachi, Jami'ar Lahore, dama wasu shahararrun jami’o’I.
Facebook Forum