Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wacce Rawa Mata Za Su Iya Takawa a Siyasar Najeriya?


Mata a harkoin siyasa na da mahimmanci
Mata a harkoin siyasa na da mahimmanci

Cibiyar bunkasa harkokin demokaradiyya ta National Democratic Institute na Muradin aiki tare da masu ruwa da tsaki musamman kafofin yada labaru domin aiwatar da shirin ta na fafutikar baiwa mata damar shiga a dama da su cikin harkokin siyasa a Nigeria

Cibiyar ta National democratic Institute NDI wadda ta shafe shekaru 30 tana aikin tallafawa mata shiga harkokin siyasa a kasashen duniya daban daban, na kokarin wayar da kan al’umma game da muhimmancin rawar da mata kan taka wajen ci gaban demokaradiyya.

A karkashin shirinta mai lakabin Women In Politics, wadda hukumar raya kasashe ta Burtaniya DFID ke samar da kudaden aiwatar dashi, NDI ta himmatu wajen ganin adadin mata masu mukaman siyasa ya karu a jihohin Kano da Jigawa da Kaduna da Adamawa da Anambra da Enugu da kuma Lagos.

Dr Mustafa Muhammad na kungiyar DAG masu aiki tare da cibiyar NDI yace an yi bincike aka gano kowane bangare na da nashi matsalar. Kamar yankin arewa maso yammacin Nigeria idan an zo batun da ya shafi mata ko fyade da ake yiwa kananan yara babu mace daya da za ta ba da nasu bangaren. Duk abun da ya shafi mata ‘ya mace ce za ta gane.

Malam Bashir Muhammad Bashir Masani ne kan lamuran sadarwa da harkokin yada labarai, na cikin wadanda suka halarci taron. Yace wannan babban al’amari ne wanda yak e da sarkakiya kwarai da gaske. Kafofin yada labarai na da alfanu saboda ta hanyarsu ne mutane za su gane yadda za’a shigar da mata a dama dasu. Akwai matan da Allah ya basu ilimi da wayewa idan suka shiga cikin harkokin mulki akwai rawar da za su taka koda kafofin labarai sun wayar da kawunan mutane amma idan mazajensu basu yadda ba babu abun da za’a yi

Baya ga ‘yan jarida, yanzu haka a cibiyar ta NDI ta dukufa wajen neman hadin kan malamai da jam’iyyun siyasa da kuma majalisun dokokin na jihohi. To amma comrade Yahaya Shu’aibu Ungogo dake sharhi kan al’amuran yau da kullum yace, “ba wani addini da ya hana mace rike wani abu da zai zama da anfani ga al’umma muddin ta na da ilimin da za ta yi haka. Amma babban abun da kowa ya ke tsoro shi ne raunin mata. Sai dai wane irin rauni ne ya fi na ‘yan siyasa da ke canza sheka sau biyu sau uku cikin shekara guda? Su kansu maza ‘yan siyasa ba tunanen mutane suke yi ba, sai na kansu. Ba sa tunanen wasu mata. Ana tafiya tar maza da matan amma matan ne suke bauta masu… Maza sun kakkame duk inda mata za su iya shiga. Sun ki sub a mace. Wannan ita ce dabi’ar mutanen da ke shugabancinmu”

Wannan yunkuri na cibiyar NDI na zuwa ne a dai dai lokacin da Jam’iyyun siyasa a Nigeria ke sayar da takardun tsayawa takarar mukamai daban daban domin tunkarar zabukan shekara ta 2019 dake tafe.

A saurari rahoton Mahmud Ibrahim Kwari

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:36 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG