Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurkawa Na Tunawa Da Harin Ta'addancin Ranar 11 Ga Satumban 2001


Harin ranar 11 ga watan Satumban 2001
Harin ranar 11 ga watan Satumban 2001

Kamar yadda Amurkawa su ka saba kowace shekara, yau ma su na alhanin mutuwar mutane wajen 3000 a harin ta'addancin nan na ranar 11 ga watan Satumban 2001.

Ranar 11 ga watan Satumban 2001, na daya daga cikin abubuwa na farko da Aiden Thayer ya fara tunawa a rayuwarsa.

Aiden na dan shekara uku kawai lokacin da ‘yan ta’addar al-Ka’ida su ka kaddamar da jerin hare hare hudu da su ka tsara kan Amurka ta wajen amfani da jiragen saman fasinja.

Biyu daga cikin jiragen sun tunkuyi dogayen tagwayen gine ginen nan na Twin Tower mai dauke da Cibiyar Cinakayyar Duniya ta World Trade Center da ke birnin New York. Jirgi na uku an rikito da shi kan ginin hedikwatar tsaron Amurka ta Pentagon da ke kusa da Washington DC, babban birnin Amurka. Amma fasinjojin cikin jirgi na uku, wanda ga dukkan alamu an karkatar da shi ne zuwa fadar Shugaban Amurka ta White House, sun yi kukan kura su ka kwace jirgin daga hannun ‘yan ta’addar su ka rikito da shi a wani fili a Pennsylvania.

Mackenzie, right, and Madison Miller from Avonmore, Pa., visit the Wall of Names at the Flight 93 National Memorial in Shanksville, Pa., Thursday, Sept. 10, 2020, as the nation prepares to mark the 19th anniversary of the Sept. 11, 2001, attacks. The Wall
Mackenzie, right, and Madison Miller from Avonmore, Pa., visit the Wall of Names at the Flight 93 National Memorial in Shanksville, Pa., Thursday, Sept. 10, 2020, as the nation prepares to mark the 19th anniversary of the Sept. 11, 2001, attacks. The Wall

Mahaifiyar Thayer ta sheka makarantarsu ta dauko shi da rana cikin matukar firgita. Ta sheka da mota zuwa gidansu da ke Springfield, Virginia, minti 15 daga Pentagon a mota. Ta zaunar da Thayer gaban TV ya yin da ta ke ta kiran mahaifinsa, Bradley Thayer, wanda ke aiki a Pentagon a ranar amma ya yi nasarar ficewa lafiya.

“Na tuna da yadda, cikin firgita, na yi ta ganin yadda gidajen talabijin ke ta nuna yadda jirgi na biyu ya yi karo da dogon gini na biyu,” a cewar Thayer, wanda a yanzu ke da shekaru 22. Ya kara da cewa, “Yanzu haka ina ta tuna yadda na yi ta ganin hoton akai akai, na yadda jirgi na biyun, wanda bai da nisa sosai, ya gwabji dogon ginin.”

A wannan ranar, mutane 2,977 sun mutu, kamar yadda su ma ‘yan al-Ka’idan 19 duk su ka mutu, a wannan harin, wanda shi ne harin ta’addanci mafi muni da aka taba kaddamarwa cikin Amurka.

Yau shekaru 19 da faruwar al’amarin, Thayer na cikin shekarunsa na biyar a Jami’ar Western Reserve ta Ohio. Thayer, duk da iya tuna abubuwan da su ka jibanci hotuna, bai iya tuna abubuwa da dama game da ranar da hare haren nan su ka auku.

Ga Amurkawan da su ka girme shi kuwa, wannan al’amari na ranar 11 ga watan Satumba, abu ne da har yanzu su ke iya tuna shi kusan dalla dalla. Shekaru 10 bayan wannan al’amari, har yanzu kashi 97% na Amurkawa masu shekaru 8 zuwa sama a lokacin da abin ya faru, su na iya tuna ainin inda suke a lokacin da su ka ji labarin aukuwar abin, bisa ga binciken da cibiyar Pew ta yi.

Tuni dai Shugaban Amurka Donald Trump da dan takarar Shugaban kas ana jam’iyyar Demokarat Joe Biden su ka bi sahun sauran Amurkawa wajen tunawa da mutane kusan 3,000 da su ka mutu a hare haren.

Shugaba Trump ya yi jawabi yau Jumma’a a shirayin tuni na Flight 93 da ke Shanksville, Pennsylvania, inda fasinjoji 40 su ka mutu. Biden kuma ya je gidan adana kayan tarihi na 9/11 da ke Birnin New York. Daga bisani zai zarce Shanksville shi ma.

Trump 9-11 Anniversary
Trump 9-11 Anniversary

“Yau, mu na masu girmama sadaukar da ransu da su ka yi, kuma mu na masu matukar juyayin kyawawan rayuka wajen 3000 da aka raba mu da su a ranar 11 ga watan Satumban 2001,” a cewar Trump.

Shi kuwa Biden cewa ya yi, “Yau dai babu wani abin labari da zai yi. Ba abin da zan ce illa batun harin 9/11. Mun tsai da dukkan tallace tallacenmu na siyasa. Ranar bakin ciki ce…”

Democratic presidential candidate former Vice President Joe Biden greets Vice President Mike Pence at the 19th anniversary ceremony in observance of the Sept. 11 terrorist attacks at the National September 11 Memorial & Museum in New York, on Friday, Sept
Democratic presidential candidate former Vice President Joe Biden greets Vice President Mike Pence at the 19th anniversary ceremony in observance of the Sept. 11 terrorist attacks at the National September 11 Memorial & Museum in New York, on Friday, Sept

Dan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar Demokarat, Joe Biden na gaisawa da Mataimakin Shugaban Amurka Mike Pence a harabar ginin ajiye kayan tarihi na tunawa da wadanda hare haren ranar 11 ga watan Satumban 2001 su ka rutsa da su.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG