Umra’u Aliyu matashiya ce da ta karanci Business Administration wato Ilimin kasuwanci a jami’ar Ahmadu Bello dake Zaria. Amma a maimakon haka ta so ta karanci Accounting wato fannin ajiya da lissafin kudi, sai dai a lokacin bata samu dama ba.
Kasan cewar hukumar da ke kula da jami’u bata ba jami’ar Ahmadu Bello damar daukar wannan kwas din ba, a cewar ta wannan shi ne dalilin da ya sa bata karanci kwas din da ta so ba, maimakon haka ne ta karanci kwas din da ke kusanci da shi.
Dan gane da kalubale kuwa ta ce yau da gobe sai Allah, ta dan fuskanci matsaloli mussamman na neman wajen zama, hada-hadar karatu, sayan takardun hannu, da sauran su, waddanan na daga cikin matsalolin da mafi akasarin dalibai kan fuskanta.
Ta kara da cewa ko ba komai a yanzu tana amfani da karatun da ta yi, domin kuwa ta karanci harkar kasuwanci, don haka bayan aikin gwamnati da take yi, tana kuma wasu sana’o'in da ba’a rasa ba, domin zama mai dogaro da kai.
Malama Umra'u ta ce tayi wa kasa hidima a jihar Yobe, ko da yake a lokacin ana fuskantar matsalolin kungiyar Boko Haram, don haka ne aka canza mata jiha inda ta koma babban birnin tarayya na Abuja domin yiwa kasa hidima.
A saurari cikakken hirar su da wakiliyar DandalinVOA Baraka Bashir.
Facebook Forum