Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya zargi Amurka da yunkurin yin babakere a fannin huldar kasa da kasa, sai dai yace har yanzu a shirye Rasha take ta bada hadin kai.
Ya bayyana haka ne jiya Alhamis a wani shirin talabijin na tambayoyi da amsoshi a Rasha, inda ya rika amsa tambayoyin jama’a.
Da yake ambatan Amurka a kaikaice, Mr Putin yace, wadansu manyan kasashe masu ikon fada a ji dake daukar kansu a matsayin wadanda suka fi kowa iko a duniya, suna son ‘yan amshin shata ne ba abokan kawance ba”
Yace bayan yakin duniya na biyu, Moscow tayi kokarin amfani da karfi wajen cusa tsarinta na bunkasa kasa kan kasashen gabashin Turai da dama, kuma babu wani alherin da wannan ya haifar. Yace abinda Amurka take yi ke nan yanzu,ta wajen tilaswa duniya bin tsarinta, ya kara da cewa, suma hakarsu ba zata cimma ruwa ba.
Shugaban kasar Rashan yana mai ra’ayin cewa, Amurka ta tilastawa wadansu shugabannin kasashen Turai kada su halarci bukukuwan da za’a gudanar a Moscow ranar tara ga watan Mayu na tunawa da cika shekaru hamsin da kawo karshen yakin duniya na biyu a kasashen Turai.
Da aka tambayi tsohon firai ministan Lithuaniya Andrius Bubilius kan furucin Mr Putin cewa Amurka tana neman ‘yan amshin shata, sai ya shaidawa Muryar Amurka cewa, mai yiwuwa ne shugaban kasar Rashan yana tunanin yadda yake son ganin dangantakarsa da makwabtansa ne.