Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Uganda Ta Tabbatar Da Bullar Cutar Ebola, Da Mutuwar Mutum Guda


Bullar Cutar Ebola a babban birnin Kampala na Uganda
Bullar Cutar Ebola a babban birnin Kampala na Uganda

Uganda ta tabbatar da barkewar annobar Ebola a Kampala, babban birnin kasar, inda mutumin farko da aka tabbatar yana dauke da cutar ya mutu a jiya Laraba, kamar yadda ma’aikatar lafiyar kasar ta bayyana a yau Alhamis

Wannan shine karo na 9 da kasar dake gabashin Afrika ke samun barkewar annobar tun bayan da cutar da kwayoyin virus ke yadawa ta fara bulla an Uganda a 2000.

An tabbatar da bullar cutar Ebola a Kampala babban birnin Uganda
An tabbatar da bullar cutar Ebola a Kampala babban birnin Uganda

Mutumin daya kamu da cutar, wanda ma’aikacin jinya ne dake aiki da babban asibitin kasar dake birnin Kampala mai suna “Mulagp National Referral Hospital”, ya fara neman lafiya a asibitoci da dama ciki harda na Mulago, dama wani mai maganin gargajiya, bayan daya fara fama da wasu alamu masu kama da zazzabi.

“Maras lafiyar ya gamu da gazawar muhimman gabobi da dama sannan ya mutu sakamakon cutar a babban asibitin na mulago a jiya 29 ga watan Janairun da muke ciki. Binciken da aka gudanar a kansa bayan mutuwa ya nuna cewa yana dauke da nau’in kwayoyin cutar virus dangin Sudan Ebola,” kamar yadda ma’aikatar lafiyar kasar ta bayyana a cikin wata sanarwa.

Allurar rigakafin cutar Ebola
Allurar rigakafin cutar Ebola

An dauki bayanan mutane 44 da ya yi mu’amala dasu domin nemo su, ciki har da ma’aikatan jinya 30, a cewar ma’aikatar.

-Reuters

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG