Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mbappe Ya Zura Kwallonsa Ta Farko Da Real Madrid A Gasar UEFA


Kylian Mbappe
Kylian Mbappe

Kwallon ta bai wa Madrid jagora da ci 1-0, amma Stuttgart ta farke ta hannun Deniz Undav a minti na 68.

Kylian Mbappé ya zura kwallonsa ta farko a gasar Zakarun Turai tare da Real Madrid a ranar Talata yayin da ya ci gaba da neman lashe kofin Turai.

Mbappé ya sami damar zura kwallo a raga bayan wata harbor kwallo da Rodrigo ya yi cikin ‘yan daƙiƙu bayan hutun rabin lokaci a karawar ta Madrid da Stuttgart a filin wasa na Santiago Bernabeu.

Kwallon ta bai wa Madrid jagora da ci 1-0, amma Stuttgart ta farke ta hannun Deniz Undav a minti na 68.

Mbappé ya kasance shiru mafi yawancin lokacin kafin nan, tare da samun damar yin kwallo a minti na 25 bayan ya shiga cikin yankin.

A karshen wasan Madrid ta doke Stuttgart da ci 3-1. Edrick da Rudiger sun kara kwallaye guda-guda.

Dandalin Mu Tattauna

Kofin Duniya ta Qatar 2022

Kofin Duniya ta Qatar 2022
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:32 0:00
Karin bayani akan Kofin Duniya ta Qatar 2022

Ronaldo vs. Messi

Ronaldo vs. Messi
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:01:24 0:00
Satumba 30, 2020

Ronaldo vs. Messi

Karin bayani akan Wasanni
XS
SM
MD
LG