Hadaddiyar Daular Laraba ta ayyana cewa tana neman wasu ‘yan Najeriya shida da take zargi da hannu a ayyukan ta’addanci.
Jaridar yanar gizo ta Al Arabiya ta ruwaito kamfanin dillancin labaran kasar na WAM yana cewa ‘yan Najeriyar da ake nema, na daga cikin mutum 38 da daular ta Laraba ta ayyana ta ayyana sunayensu a matsayin wadanda ake nema ruwa a jallo.
Rahotanni sun ce Hadaddiyar Daular ta Laraba ta bayyana sunayen ne a wani mataki na dakile ayyukan masu daukan nauyin ‘yan ta’adda.
Jaridar ta Al Arabiya ta ce mutum 38 da ake nema, hudu daga cikinsu ‘yan kasar ta daular larabawa ne, biyu ‘yan Lebanon, takwas ‘yan Yamal, biyar ‘yan Syria.
Sannan har ila yau ta ce, biyar daga cikinsu ‘yan Iran ne, shida ‘yan Najeriya, biyu ‘yan Iraqi sai mutum dai-dai a India, Afghanistan, Birtaniya, Saint Kitts-Navis, Rasha da Jordan.
Idan ba a manta ba, a watan Nuwambar bara ma, wata kotu a kasar ta Daular Larabawa ta yankewa wasu ‘yan Najeriyar shida hukuncin daurin zaman gidan yari bayan da aka same su da laifin samar da kudade ga ‘yan ta’adda.
Ko da yake, abokanan huldarsu sun ce kudaden da suka tura da yawansu ya kai dalar Amurka dubu 782, 000 daga Dubai zuwa Najeriya a tsakanin 2015 zuwa 2016 ba na ayyukan ta’adanci ba ne.
Ga sunayen mutanen da jaridar ta Al Arabiya ta wallafa kamar yadda kamfanin dillancin labarai na WAM ya ruwaito:
1. Ahmed Mohammed Abdulla Mohammed Alshaiba Alnuaimi (UAE)
2. Mohamed Saqer Yousif Saqer Al Zaabi (UAE)
3. Hamad Mohammed Rahmah Humaid Alshamsi (UAE)
4. Saeed Naser Saeed Naser Alteneiji (UAE)
5. Hassan Hussain Tabaja (Lebanon)
6. Adham Hussain Tabaja (Lebanon)
7. Mohammed Ahmed Musaed Saeed (Yemen)
8. Hayder Habeeb Ali (Iraq)
9. Basim Yousuf Hussein Alshaghanbi (Iraq)
10. Sharif Ahmed Sharif Ba Alawi (Yemen)
11. Manoj Sabharwal Om Prakash (India)
12. Rashed Saleh Saleh Al Jarmouzi (Yemen)
13. Naif Nasser Saleh Aljarmouzi (Yemen)
14. Zubiullah Abdul Qahir Durani (Afghanistan)
15. Suliman Saleh Salem Aboulan (Yemen)
16. Adel Ahmed Salem Obaid Ali Badrah (Yemen)
17. Ali Nasser Alaseeri (Saudi Arabia)
18. Fadhl Saleh Salem Altayabi (Yemen)
19. Ashur Omar Ashur Obaidoon (Yemen)
20. Hazem Mohsen Farhan + Hazem Mohsen Al Farhan (Syria)
21. Mehdi Azizollah Kiasati (Iran)
22. Farshad Jafar Hakemzadeh (Iran)
23. Seyyed Reza Mohmmad Ghasemi (Iran)
24. Mohsen Hassan Kargarhodjat Abadi (Iran)
25. Ibrahim Mahmood Ahmed Mohammed (Iran)
26. Osama Housen Dughaem (Syria)
27. Abdurrahaman Ado Musa (Nigeria)
28. Salihu Yusuf Adamu (Nigeria)
29. Bashir Ali Yusuf (Nigeria)
30. Muhammed Ibrahim Isa (Nigeria)
31. Ibrahim Ali Alhassan (Nigeria)
32. Surajo Abubakar Muhammad (Nigeria)
33. Alaa Khanfurah - Alaa Abdulrazzaq Ali Khanfurah - Alaa Alkhanfurah (Syria)
34. Fadi Said Kamar (Great Britain)
35. Walid Kamel Awad (Saint Kitts and Nevis)
36. Khaled Walid Awad (Saint Kitts and Nevis)
37. Imad Khallak Kantakdzhi (Russia)
38. Mouhammad Ayman Tayseer Rashid Marayat (Jordan)