Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Akawu Na Farko Dan Asalin Najeriya Akintola Williams Ya Rasu.


Akawu Na Farko Dan Asalin Najeriya Akintola Williams.
Akawu Na Farko Dan Asalin Najeriya Akintola Williams.

Williams, mai shekaru 104, ya rasu ne a cikin barcinsa da sanyin safiyar yau Litinin, 11 ga watan Satumba.

WASHINGTON, D. C. - An fi sanin Williams ne da Doyen mai sana’ar akawu a Najeriya, ya kuma taka rawar gani wajen bunkasa harkar hada-hadar kudi ta kasar.

Williams ya karanci lissafin kudi a Jami'ar London kuma ya samu mukami na matsayin babban akawu wato Chartered Accountant a shekarar 1947.

Bayan komawarsa Najeriya a shekarar 1952, ya kafa kamfaninsa na lissafin kudi, Akintola Williams & Co., wanda a yanzu ake kira Deloitte & Touche.

Ya kasance Shugaban Cibiyar Chartered Accountants of Nigeria (ICAN) daga shekarar 1963 zuwa 1965 kuma yana daya daga cikin wadanda suka kafa ta.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG