Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tsohon Editan BBC Isa Abba Adamu Ya Rasu


Marigayi Isah Abba Adamu, tsohon Editan sashen Hausa na BBC
Marigayi Isah Abba Adamu, tsohon Editan sashen Hausa na BBC

Rahotannin daga ciki da wajen Najeriya sun bayyana cewa Allah ya yiwa fitaccen dan jarida kuma tsohon editan sashen hausa na BBC, Isa Abba Adamu rasuwa a ranar Lahadi bayan fama da gajeriyar jinya a birnin Landan.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya, NAN, ya ruwaito dan uwan marigayin, Malam Yusha’u Ibrahim, yana ba da sanarwar rasuwar Isah Abba Adamu, inda ya bayyana cewa, za’a yi jana’izarsa kamar yadda addinin musulunci ya tanada a birnin Landan.

Marigayi Isah Abba Adamu, wanda aka haifa a shekarar 1961, tsohon ma’aikacin gidan talabijin na Jihar Kano wato CTV ne, kafin ya koma Sashen Hausa na BBC da aiki.

Haka kuma, marigayin ya kamalla karatun digirinsa na farko a jami’ar Bayero da ke jihar Kano a shekarar 1985 wanda daga bisani ya shiga aikin jarida gadan-gadan inda ya rike mukamai da dama a BBC Hausa daga matakin furodusa har zuwa na edita.

Bayan barinsa aiki a BBC hausa, marigayi Isa Abba Adamu ya koma aiki a cibiyar nazarin dokoki da ke birnin tarraya Abuja a matsayin darakta, kuma daga baya ya ajiye aiki ya sake komawa birnin Landan.

Shugaba Muhammadu Buhari bayan darewa kan kujerar mulkin Najeriya, ya ya nada shi mamba na kwamitin amintattun kamfanin dillacin labaran Najeriya wato NAN.

Marigayi Isa Abba Adamu ya rasu yana da shekaru 60 a duniya kuma ya bar mai dakinsa da ’ya’ya hudu.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG