Sun gudanar da zanga zangar ce a harabar ma'aikatar kananan hukumomin jihar wadda saura kadan ta zame tarzoma.
Kansilolin sun share yinin jiya Litinin suna tsare da wasu manyan sakatarorin ma'aikatar a wani dakin taro.
Onarebul Yahaya Shehu shugaban kungiyar tsoffin kansilolin na jihar yace sun tsare manyan sakatarorin ne domin basu gamsu da bayanin da suka basu ba. Yace kowanene zasu kira su kira amma su suna son kudinsu domin sun gaji da jira. Yace ko kwana zasu yi ba zasu sakesu ba sai an biyasu hakinsu. Tunda suka shiga ofisoshinsu har suka gama ba'a biyasu ba. Yanzu sun yi wata takwas da sauka amma shiru ka ke ji.Yace kowannensu yana bin gwamnatin jihar nera miliyan uku da dubu dari biyar. Tsoffin kansilolin su dari biyu da saba'in da hudu ne-274.
Wasu kansilolin sun yi karin haske akan batun. Sun ce wasunsu an kaisu kara saboda basussuka dake kansu.
Sakataren gwamnati Alhaji Idris Indako ya mayar da martani. Yace babu abun da zasu iya yi yanzu domin idan sun biya albashi ba zasu iya biyan kansilolin ba. Zanga zangar ta cigaba.
Ga rahoton Mustapha Nasiru Batsari.