Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasu Sun Yi Yunkurin Sace Sandar Majalisar Dattawan Najeriya


Yunkurin da aka yi na sace sandar majalisar dattawa
Yunkurin da aka yi na sace sandar majalisar dattawa

An samu hargitsi a Majalisar Dokokin Najeriya inda wasu ‘yan daba suka shiga zauren Majalisar suka dauki sandar girma.

A yau Laraba ne lokacin da zaman Majalisar Dattawa ke zamanta, wasu da ba a san ko su waye ba suka kutsa cikin zauren Majalisar suka ‘dauki sandar girma, wadda itace sandar iko dake basu hurumin yin zama da samar da dokokin da zasu shafi ‘yan Najeriya.

An bayyana ‘yan dabar da cewa magoya bayan Sanata Ovie Omo-Agege, wanda ya fito daga yankin Niger-Delta da Majalisar ta dakatar a makon da ya gabata.

Bayan kwashe lokaci ana kokawa a zauren Majalisa an sami nasarar kwace sandar, san nan Majalisa ta koma zamanta.

Ganin cewa ginin Majalisa waje ne mai cike da tsaro hakan yasa ya zamanto abin mamaki kan yadda wadannan mutane suka sami nasarar shiga zauren.

Yanzu haka dai an rufe duk kokafin shiga ginin Majalisa tare da tantance duk masu shiga da fita don tabbatar da tsaro.

Domin karin bayani saurari hira da wakilyar Muryar Amurka Medina Dauda.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:49 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG