Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Trump Yana Neman Goyon bayan Soke Dokar ‘Yancin Zama Dan Kasa Ta Haihuwa.


Shugaban Amurka Donald Trump
Shugaban Amurka Donald Trump

Shugaban Amurka Donald Trump yana kara gangami a kan yunkurinsa na soke dokar da take baiwa yaran da aka haifa a Amurka ‘yancin zama dan kasa, yayin da dubban bakin haure suke karasowa a hankali zuwa iyakar kudancin Amurka.

Da yake jawabi a wurin taron gangamin siyasa da yammacin shekaranjiya Laraba kafin zaben rabin wa’adi mako mai zuwa, Trump ya yi kokarin neman goyon bayan jama’a a kan shawarar da ya yanke ta soke dokar ‘yancin zama dan kasa ta haifuwa.

Yace a cikin lokaci kalilan idan suka shigo kasar mu, ‘ya’yan daruruwar bakin hauren da basu da iznin zaman kasar za su zama ‘yan kasa kai tsaye saboda wannan dokar marar ma'ana, kuma nan take sai su samu damar cin kowane amfani da duk wani ba-Amurke zai samu na biliyoyin dala a kowace shekara.

Trump ya kuma ce zai aika da sojoji dubu 15 a kan iyakar kasar da Mexico domin hana ayarin bakin haure daga tsakiyar nahiyar Amurka, wadanda suke niyar shigowa Amurka ba bisa ka’ida ba shiga kasar .

Trump ya bayyana bakin hauren a matsayin mutanen da ya kamata aji tsoronsu. Koda yake akasarin bakin hauren suna cewa suna so su shiga Amurka ne domin gujewa tashin hankalin kuma su samu rayuwa mai iganci da basu samu a kasarsu.


  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG