Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Trump Ya Nuna Rashin Jin Dadinsa Ga Shugaban Ma'aikatar Shari'a Ta Amurka


Shugaba Trump ya sha nanata cewa babu wata alaka tsakanin kwamitin kamfen dinsa da jami'an Rasha.

Shugaban Amurka Donald Trump ya fadawa jaridar New York Times cewa in har babban Jami’i mai bincike na musamman da ke binciken rawar da Rasha ta taka a zaben shugaban kasa da aka yi cikin shekarar da ta gabata, da kuma yiwuwar jami’an kempe din sa sun gana da jami’an Rasha, ya fadada bincikensa zuwa duba harkokin kudaden iyalin Trump din, wanda bai da alaka da Rasha, za’a iya daukar cewa binciken nasa yana neman ya wuce gona da iri.

Trump ya ce “lallai zan ce tabbas ya wuce din” a lokacin da aka tambaye shi ko hakan ya wuce gona da iri? a cewar wani rubutaccen bayani da aka fidda jiya Laraba. Trump ya kuma ce ba ya da wata hanyar samun kudi daga Rasha, don ba ya wata harkar kasuwanci a Rasha.

A wata hira da aka yi da shi inda ya tabo batutuwa dabam-dabam, shugaban ya bayyana rashin jin dadinsa akan matakin da Babban jigon shari’a na Amurka, Attorney Janar Jeff Sessions ya dauka na fidda kansa daga binciken Rasha, inda Trump yace da tun farko Sessions ya nuna alamun daukar wannan matakin kafin a nada shi, da Trump bai zabe shi ba, ya nada wani akan mukamin.

Haka kuma Trump kuma ya nuna cewa tsohon shugaban hukumar binciken FBI James Comey ya nuna masa wasu bayannan sirri game da shi Trump din don ya razana shi, shi kuma ya sami damar cigaba da rike mukaminsa.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG