Shugaban Amurka Donald Trump, na kokarin bayyana wani kudurin doka da zai rage adadin mutanen da ke shiga kasar bisa ka’ida, tare da hadin kan wasu sanatoci ‘yan jam’iyar Republican biyu da suka tattauna da shugaban a Fadar White House.
A farkon shekarar nan, Sanata Tom Cotton da David Perdue suka gabatar da wata doka da za ta rage adadin bakin da ke shiga kasar daga miliyan daya zuwa dubu 500 a kowace shekara.
Kudirin har ila yau, zai nemi rage adadin ‘yan uwan bakin da ke shiga kasar, da kawo karshen shirin tambola na lottery da kuma tsaurara matakan samun katin zama a Amurka na dindindin, wato Green Card.
Sau biyu Trump yana ganawa da sanatocin kan wannan kudirin dokar, wanda yunkuri ne na cika daya daga cikin alkawuran da ya yi na kawo sauyi a fannin shige da ficen kasar.
Facebook Forum