An mayar da bikin rantsar da zababben Shugaban Amurka Trump zuwa rufaffan wuri saboda matsanancin sanyin da ake hasashen za’a yi a birnin Washington DC, kamar yadda majiyoyi da dama da ke da masaniya ta kai tsaye game da shirin suka shaidawa tashar talabijn ta CNN.
Ana shirin rantsar da Donald Trump da zababben matamakin shugaban kasa kan mukamansu a cikin babban dakin taro na Majalisar Dokokin Amurka, a cewar majiyoyin.
Har yanzu ana ci gaba da mahawara akan wurin da za’a gudanar da faretin rantsarwar da sauran shagulgulan bikin.
Sai dai, tawagar Shugaba Trump na tattaunawa a kan yiyuwar gudanar da wasu daga cikin bukukuwan a dandalin “Capital One” inda zai gudanar da gangami a ranar Lahadi.
Haka kuma tawagar ta Trump na tattaunawa da kwamitin hadin gwiwar Majalisar Dokokin kasar a kan yadda za’a yi da dubun dubatan mutanen da ke shirin yin balaguro domin shaida rantsar da shi daga farfajiyar da ke tsakanin fadar White House da ginin majalisar ta Capitol.
Har yanzu ana ci gaba da nazari a kan wadannan shawarwari, kamar yadda majiyoyin suka shaidawa CNN.
Jami’ai sun bayyana damuwar cewa matsanancin sanyin na iya yin barazana ga lafiyar baki da mahalarta bikin.
Ronald Regan ne shugaba na karshe da aka rantsar a rufaffen wuri a 1985, sa’ilin da ma’aunin sanyi da rana tsaka ya sauka zuwa -25.
Reagan ya karbi rantsuwar kama aiki a dakin taro na Majalisar Dokokin kasa inda aka soke faretin karbar rantsuwar.
Dandalin Mu Tattauna