A yayin gudanar da yakin neman zabensa a Nevada a ranar Assabar, Trump ya ce Amurka na matakin karshe na dakile coronavirus, batun da babban masanin cutattuka masu yaduwa Anthony Fauci ya musanta.
A wani gangamin yakin neman zabe kuma, Trump ya musanta alkaluman wadanda suka mutu a kasar 194,000 da ya zarta na ko’ina a duniya, yana cewa kamar 180,000 ne suka mutu sakamakon cutar.
Duk da cewa kusan mutun 35,000 ke kamuwa, yayin da 1,000 suke mutuwa a kowace rana a Amurka, Trump ya wallafa a shafinsa na tiwita a jiya Lahadi cewa, “ Alkaluma na yin kasa cikin sauri."
Ya kara da cewa "yawan wadanda ke mutuwa da kuma wanda ake kwantarwa a asibiti sun yi kasa sosai, hatta yawan masu kamuwa da cutar yana raguwa, duk da karin yawan gwajin cutar da ake yi fiye da kowace kasa a duniya.”
To sai dai abokin hamayyar Trump na jam’iyar Demokrat, tsohon mataimakin shugaban kasa Joe Biden, bai fita kamfen ba a ranar Asabar, amma ya fadi tun farko cewa rudin jama’a da Trump ke yi, “wata babbar yaudara ce ga Amurkawa da ta shafi rai da mutuwa. Wannan raina aiki ne, kuma abin kunya ne.”
Facebook Forum