Shugaban Amurka, Donald Trump, jiya Laraba, ya ce Amurka na da zabi da dama, baya ga matakin soji, muddun ta tashi mai da martani kan hare-haren makamai masu linzami da na jirage marasa matuka, da aka kai har su ka haddasa gibi na wajen rabin man da ake samarwa a Saudiyya, a karshen makon jiya.
“Mu na kan kwakkwarar turba,” abin da Trump ya gaya ma manema labarai kenan a filin jirgin saman California, akan hanyarsa ta zuwa wajen wani gangamin tara kudin yakin neman zaben.
A Saudiyyar kuma, Sakataren Harkokin Wajen Amurka Mike Pompeo, ya zargi Iran da kaddamar da abin da ya kira, “takalar neman yaki” ta wajen kai hare-haren.
Kalaman na Trump na zuwa ne ‘yan sa’o’i bayan da ya ce zai yi matukar kara ma Iran takunkumin tattalin arziki, saboda harin da aka kai kan matatun man Saudiyya, wanda Amurka ta ce Iran ce ta kaddamar.
To sai dai Shugaban Iran, Hassan Rouhani, jiya Laraba, ya ce ‘yan kasar Yemen ne su ka kai harin, a matsayin gargadi ga kasar Saudiyya kan katsalandan din da ta ke yi na jagorantar gamayyar da ke yaki da ‘yan Houthi.
Facebook Forum