Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tinubu Zai Kai Ziyara China


Shugaba Tinubu (Hoto: Facebook/Bola Tinubu)
Shugaba Tinubu (Hoto: Facebook/Bola Tinubu)

Yayin wannan ziyara, ana sa ran Tinubu zai gana da Shugaban China, Xi Jinping, inda za su rattaba hannu kan yarjeniyoyi masu muhimmanci a cewar fadar gwamnati.

Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, na shirin kai ziyara zuwa kasar China, a wani yunkuri da fadar gwamnatin tarayya ta bayyana a matsayin mataki na inganta rayuwar ‘yan Najeriya.

A cikin wata sanarwa da Kakakin fadar gwamnati, Ajuri Ngelale, ya fitar a yammacin Talata, ya bayyana cewa shugaba Tinubu zai kai wannan ziyarar don halartar taron koli na kasashen Afirka da China wanda za a yi tsakanin 4 zuwa 6 ga watan Satumba.

Tinubu shi ne shugaban kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka ta ECOWAS.

Ana sa ran Tinubu zai tattauna kan batutuwan da suka shafi zaman lafiya da tsaro a yankin a cewar Ngelale.

A yayin wannan ziyara, ana kuma sa ran cewa Tinubu zai gana da Shugaban kasar China, Xi Jinping, inda za su rattaba hannu kan yarjeniyoyi masu muhimmanci.

Haka zalika, sanarwar ta kara da cewa Tinubu zai gana da shugabannin wasu manyan kamfanonin kasar China da suka yi fice a bangarorin ayyukan noma, iskar gas, da ilimin Tauraron adan adam.

A ranar Juma’ar da ta gabata, Tinubu ya dawo daga wata takaitacciyar ziyara a kasar Faransa.

Idan wannan ziyarar ta China ta tabbata, hakan zai nuna cewa Tinubu ya kai ziyara kasashe uku cikin kasa da wata guda.

A ranar 14 ga watan Agusta, shugaban na Najeriya ya kai ziyarar Equatorial Guinea.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG