Hukumar Kula da Shige da Ficen Najeriya ta bayyana karin farashin kudin fasfo, wanda zai fara aiki ranar daya da watan Satumba. Sai dai hakan bai yi wa ‘yan kasar dadi ba, ganin cewa al’umma na fama da matsin tattalin arziki.
A wata sanarwar da hukumar shige da ficen Najeriya ta fitar, ta bayyana cewa za a samu karin kudin fasfo daga ranar daya ga watan Satumban shekarar nan saboda wasu dalilai masu tushe.
Hukumar ta ce fasfo me shafi 32 wanda ya ke da ingancin shekaru 5, farashinsa zai tashi daga Naira 35,000 zuwa 50,000 sai kuma me shafi 64 me dauke da ingancin shekaru 10, farashinsa zai daga daga Naira 70,000 zuwa 100,000.
Hukumar ta ce ba wai haka kawai tayi karin farashin fasfon ba, karin ya zama tilas ne - ta yi ne domin sabunta shi ta yadda zai yi daidai da zamani da, tsarin ICAO, da kuma saukaka samun shi, kuma hakan zai ba wa hukumar damar bude sabbin ofisoshin samar da shi cikin sauri.
‘Yan Najeriya dai na ci gaba da bayyana rashin jin dadinsu game da irin wannan kare-karen haraji da Gwamnatin kasar ke yi a wannan marra da ake ciki.
A hirarsa da Muryar Amurka, Rilwan Ladan, daya daga cikin masu sharhi kan lamuran yau da kullum, ya ce irin wannan karin farashin ba abin mamaki ba ne, idan akayi la’akari da yadda gwamnatin kasar ta mayar da hankali kan karbar harajin da talakawa basa amfana da shi don ba sa gani a kasa.
Wakiliyar Muryar Amurka ta yi kokarin tuntubar ta kula da shige da fice, sai dai hakan bai samu ba, domin ba a amsa waya da kuma sakon kar-ta-kwana da wakiliyar ta Muryar Amurka ta aika ma hukumar ba.
‘Yan Najeriya dai na ci gaba da bayyana koken halin matsin rayuwa da su ke ci.
Saurari cikakken rahoton Rukaiya Basha daga Abuja, Najeriya:
Dandalin Mu Tattauna